GADON SARAUTA: ƘASAR IRAGBIJI ZA TA GIRMAMA ALHAJI SHEHU SANI SADO DA BABBAN SARAUTAR ‘OTUNBA SOLUDERO’!

Aragbiji na ƙasar Iragbiji ya sanar da gudanar da wani babban biki na naɗin sarauta mai tarihi, domin karrama mutum saboda gudunmawarsa a fannonin shugabanci, hidima, girmamawa, al’adu, da kuma jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya.

Daga AbdulHakeem Mutiu Adejumo-Ajeseku
Kaduna, Najeriya

LABARAN BTV : Ƙasar Iragbiji, a Jihar Osun, na shirin ganin wani babban biki na sarauta mai tarihi, yayin da Mai Martaba Oba Abdur-Rasheed Ayotunde Olabomi, Odundun na IV, wato Aragbiji na ƙasar Iragbiji, ya shirya karrama Alhaji Shehu Sani Sado — Shugaban Ƙasa na ƙungiyar ‘Capacity Movement Project 2027’ — da sarautar gargajiya mai daraja ta ‘Otunba Soludero’ na ƙasar Iragbiji (wato Babban Basarake mai kula da zaman lafiya a ƙasar Iragbiji).

An tsara gudanar da wannan biki na naɗin sarauta, wanda zai kasance mai cike da kayan al’adu da tarihi, a ranar Juma’a, 27 ga watan Nuwamba, 2026. Za a gudanar da bikin ne a fadar Aragbiji na ƙasar Iragbiji, da ke garin Iragbiji, a ƙarƙashin Karamar Hukumar Boripe, Jihar Osun, Najeriya.

Bikin, wanda aka tsara zai fara da misalin ƙarfe 10:00 na safe, ana sa ran zai samu halartar sarakunan gargajiya, shugabannin siyasa, fitattun mutane, masu ruwa da tsaki a al’umma, abokan arziki, da sauran jama’a daga ciki da wajen ƙasar Iragbiji.

Bayar da wannan sarauta ta gargajiya mai daraja, wani muhimmin ci gaba ne a tarihin al’adu da sarautar ƙasar Iragbiji, inda ake ɗaukaka kyawawan dabi’u irin su girmamawa, shugabanci, hidima, da kuma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

A cikin gayyatar da ya fitar, Mai Martaba Aragbiji na ƙasar Iragbiji ya yi kira na musamman ga dukkan ‘ya’yan ƙasar Iragbiji, baƙi masu daraja, abokan arziki, da sauran jama’a baki ɗaya, da su halarci wannan taro domin shaida wannan muhimmin lokaci na tarihi a masarautar. Wannan biki na tarihi zai kasance wani babban biki na nuna al’adun sarauta, asalin al’ada, jagoranci, da kuma hadin kan al’umma, inda zai hada mutane daga sassa daban-daban domin su kasance tare wajen girmama tsoffin al’adu da gadon gargajiya na kasar Iragbiji.

BIKIN NADA SARAUTA: BAYANAN TARON

Wanda za a bai wa sarautar: Alhaji Shehu Sani Sado.

Sarautar Gargajiya: Otunba Soludero na kasar Iragbiji (Wato, Babban Basarake mai kula da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar Iragbiji).

Rana: Juma’a, 27 ga watan Nuwamba, 2026.

Lokaci: Karfe 10:00 na safe daidai.

Wuri: Fadar Mai Martaba Oba Abdur-Rasheed Ayotunde Olabomi, Odundun na IV, wato Aragbiji na kasar Iragbiji, a garin Iragbiji, Karamar Hukumar Boripe, Jihar Osun, Najeriya.

Yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen wannan muhimmin biki na sarauta, ana gayyatar jama’a baki daya da su halarci taron da yawa, domin nuna goyon baya ga wannan babban biki na al’adu da gadon gargajiya na kasar Iragbiji.

Muna rokon Allah Ya ba mu tsawon rai domin ganin wannan biki na tarihi, kuma muna fatan taron ya kasance mai cike da nasara, zaman lafiya, farin ciki, da kuma daukaka ta musamman.

HALARTARKU ZA TA KARA WA WANNAN BIKI NA SARAUTA KYAU, GIRMA, DA KUMA SHAHARA!

Leave a Reply